Connect with us

News

Dan China: Mahaifiyar Ummita Ta Bayyana A Matsayin Shaida Ta Farko Kan Kisan ’Yarta

Published

on

Dan China

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

 

 

Advertisement

An ci gaba da sauraron shari’ar dan kasar China wato Mista Geng Quanrong a gaban Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 17 da ke zamanta a unguwar Miller Road.

Ana zargin Mista Geng Quangrong ne da kisan budurwarsa, Ummmulkulsum Buhari, wacce aka fi sani da Ummita.

Advertisement

 

Mutum 412 ne suka mutu a hatsarin ababen hawa cikin wata 10 a Legas – FRSC

Advertisement

A zaman kotun na ranar Laraba, lauyoyin gwamnati bisa jagorancin Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano Barista Musa Abdulahi Lawan, sun gabatar da shaidarsu ta farko mai suna Fatima Zubairu mai kimanin shekara 43 wacce ita ce mahaifiya ga Ummita, wanda ake zargin dan kasar Sin din da caccaka mata wuka a ranar 16 ga watan Satumba 2022 wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwarta.

Kotu ta tambayi mahaifiyar Ummulkursum ko ta yaya ta san Quarong, inda ta ce ta san shi ne sakamakon zuwa wajen ’yarta da yake yi har gida.

Advertisement

Aminiya ta ruwaito cewa ana cikin yi wa Fatima tambayoyin ne mai shari’a ya tafi hutun muntuna 15.

Muna tafe e da karin bayani…

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending