News
Mun biya malaman Jami,oi hakkin su ministan ilimi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Ministan ilimi na tarayyar Nigeria adamu adamu yace suna nan kan bakar su na kin biyan malaman ja,mio hakkin,su
a Yayin da Kuma Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ke gudanar da zanga-zangar lumana a faɗin jami’o’in ƙasar domin nuna rashin jin daɗinsu game da rashin biyansu albashin watannin da suka kwashe suna yajin aiki, gwamnatin ƙasar ta ce ba za ta biya malaman albashin aikin da ba su yi ba.
Adamu ya bayyana haka ne a ranar Laraba bayan taron majalisar zartarwa da shugaban ƙasar ya jagoranta a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja babban birnin ƙasar.
Dan China: Mahaifiyar Ummita Ta Bayyana A Matsayin Shaida Ta Farko Kan Kisan ’Yarta
Yayin da yake martani game da iƙirarin da shugaban ASUU ya yi na cewa gwamnati na son mayar da malaman jami’ar ma’aikatan wucin-gadi, ministan ya ce gwamnatin ba ta da wannan niyyar.“
An janye yajin aiki, kuma gwamnati ta biyasu haƙƙin iya aikin da suka yi. Ina tunani wannan shi ne matsayin gwamnati, cewa ba wanda za a biya albashin aikin da bai yi ba, sun yi aiki na kwanaki, kuma gwamnati ta biya su haƙƙinsu kwanakin da suka yi”, in ji ministan ilimi adamu adamu
SOURSE BBC Hausa
