Connect with us

News

Matar Da Mijinta Ya Daure Ta A Daki Ta Rasu A Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Sadiya Amin, matar da mijinta ya daure ta a daki tsawon watanni ta rasu a asibiti da aka kwantar da ita.

 

Advertisement

A daren Lahadi ne daya daga cikin masu jinyarta tare da taimaka mata, a karkashin Gidauniyar Adamu Abubakar Gwarzo Foundation, Musa Abdullahi Sufi ne ya sanar da rasuwar ta shafinsa na Facebook.

 

Advertisement

Shirin Noman Rani Na Biliyoyin Naira A Dam Din Gurara Ya Zama Shifcin Gizo – Manoma

Ana zargin mijin marigiyar ya kulle ta a daki cikin tsananin rashin lafiya, bai kai ta asibiti ba, sai dai ya ba ta koko da naman hazbiya kamar yadda muka ba ku labari a kwanakin baya.

Daga bisani mahifiyarta da ta kai ziyara inda take da dawo da ita Kano, bayan ta ga halin da ta ke ciki.

Advertisement

 

Kwnanaki kadan da kawo ta Kano, mahaifinta ya rasu, wanda cewar Abdullahi Sufi ya ce na da alaka da ganin halin da ’yar sa ta shiga.

Advertisement

Fitacceen dan gwagwarmayar ya ce ba za su kyale lamarin ba, sai sun dauki matakin da ya dace wajen bi wa marigayiyar hakkinta.

 

Advertisement

“Yanzu za mu dukufa wajen nemo wa Sadiya hakkin ta wajen wannan miji da ya zalunce ta,” in ji shi.

 

Advertisement

Ya kuma yi kira ga jama’a da su yi hattara da wasu kungiyoyi da mutane da ke neman tallafi da sunan marigayiya Sadiya.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending