Connect with us

News

Jihar Kano Ta Sake Samun Sabon Kwamishinan Yan Sanda.

Published

on

 

Babban sifeton yan sanda, Usman Alkali Baba, ya turo CP Ahmad Kontagora, zuwa Kano a matsayin sabon kwamishinan yan sanda da zai jagoranci gudanar da zaben gwamna da na yan majalisar dokoki na jiha.

Advertisement

Wannan ya biyo bayan dakatar da turo CP Feleye Olaleye, da babban sifeton yan sandan ya yi, bayan an turo a makon da ya gabata a kwamishinan yan sandan jihar.

Mai Ilimine Kadai Zai,iya Jogorancin ƙaramar Hukumar Dala…. Hon Bandirawo

A yan kwanakinnan dai rundunar yan sandan ta turo kwamishinonin yan sanda akai-akai zuwa jihar Kano, wanda ya janyo korafi da gudanar da zanga-zanga daga magoya bayan jam’iyyar adawa ta NNPP, sakamakon yunkurin turo tsohon babban jami’in tsaron gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje wato CP Balarabe Sule, wanda shi ma aka dakatar da turo shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending