Connect with us

News

Ghana za ta fara amfani da zinare wajen sayen man fetur a maimakon kuɗi

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Mataimakin shugaban ƙasar Ghana Mahamudu Bawumia ya ce gwamnati na duba yiwuwar yadda ƙasar za ta rinƙa amfani da zinare wajen sayen man fetur ɗin da take shigowa da shi ƙasar a maimakon kuɗaɗen waje.

Advertisement

Kotu ta dakatar da gwamnatin tarayya daga ƙirƙiro kamfanin jirgin sama na ƙasa, Nigeria Air.

Jaridar Pulse ta ruwaito Bawumia na cewa matakin wani yunƙuri ne na magance faɗuwar da darajar takardar kuɗin ƙasar ke yi babu ƙaƙƙautawa da kuma tashin farashin kaya.

A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na facebook, ya ce “gwamnati na tattaunawa kan wani tsari ta yadda za mu rinƙa amfani da zinarenmu (a maimakon dalar Amurka) wajen sayen man fetur.”

Advertisement

Jaridar ta ruwaito cewa tsarin zai fara aiki ne a ƙarshen watanni uku na farko na shekarar 2023.

Bawumia ya ce “idan tsarin ya fara aiki, zai rage abin da muke kashewa, sannan zai rage ci gaban faɗuwar darajar kuɗinmu wanda ake alaƙantawa da tashin farashin mai, da ƙarfin lantarki, da ruwa, da sufuri da abinci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending