News
Gwamnonin jihohi ne suka jefa Najeriya cikin talauci, in ji gwamnatin Tarayya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dora alhakin katutun talaucin da ke damun kasar kan gwamnonin jihohi.
Karamin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare, Clem Agba ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya ranar Laraba, kamar yadda gidan talbijin na Channels TV ya rawaito.
Gwamnati ta amince a fara amfani da harshen Hausa wajen koyar da ‘yan firamare
Ya ce shirin gwamnatin tarayya na kyautata rayuwar ‘yan kasar bai yi tasirin da ya kamata ba ne saboda gwamnonin jihohi ba su bai wa gwamnatin tarayya hadin kai ba.
Mr Agba ya kara da cewa gwamnonin sun fi mayar da hankali wajen aiwatar da ayyukan da ba su da muhimmanci, maimakon inganta rayuwar al’ummar karkara.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
