Connect with us

News

Mahaifiya Ta Binne Jaririyar Da Ta Haifa Ranta A Cikin Masai

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

An kama wata mata mai kimanin shekara 30 da ke kauyen Tsurma a Karamar Hukumar Kiyawa ta jihar Jigawa bisa zargin binne jaririyar da ta haifa a cikin masai.

 

Advertisement

Da yake tabbatar da kamen, Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Lawan Shi’isu, ya ce tuni suka tono gawar jaririyar sannan suka cafke wacce ake zargin.

Arzikin Aliko Dangote ya ƙaru da dala biliyan 1.5 a watan Nuwamba

 

Ya kuma ce, “Bayan samun rahoton, mun aike da jami’anmu zuwa wajen, inda suka tono gawar daga cikin masan da ake zargin a ciki ta binne jaririyar.

 

“Yanzu haka mun cafke matar kuma tana hannunmu,” inji Lawan.

 

Advertisement

 

Kakakin ya kuma ce an garzaya da gawar Babban Asibitin Dutse, inda likita ya tabbatar da rasuwarta.

 

Ya kuma ce bincikensu na farko-farko ya kai su ga kama wani mai suna Amadu Sale da aka fi sani da Dan Kwairo mazaunin kauyen Akar a Karamar Hukumar ta Kiyawa, wanda shi ake zargi tun farko da yi mata cikin shege.

 

Ya ce bayan yi mata cikin, an zargi Dan Kwairo da hada baki da ita domin ta kashe yarinyar bayan ta haife ta.

Advertisement

 

Kakakin ya kuma ce tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Emmanuel Ekot, ya ba da umarnin mayar da lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar domin fadada bincike.

 

Ya ce da zarar an kammala binciken, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya domin su girbi abin da suka shuka

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending