Connect with us

News

Likitoci sun roƙi Musaveni ya tsaya takarar shugaban Uganda a karo na bakwai

Published

on

Yoweri Musaveni

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Wasu gungun likitoci a Uganda sun haifar da cece-ku-ce bayan da suka durƙusa a gaban shugaban ƙasar Yoweri Musaveni suna roƙon sa ya tsaya takarar shugaban ƙasa a karo na bakwai.

Matakin G7 Na Karya Farashin Man Rasha Ya Fara Aiki

Musaveni mai shekara 78 ya kasance kan mulki tun shekarar 1986. Sannan za a gudanar da zaɓen ƙasar na gaba ne a shekarar 2026.

Likitocin ƙarƙashin Ƙungiyar likitoci ta Uganda (UMA) suna halartar wani taro ne kan kishin ƙasa a Kampala, babban birnin ƙasar, lokacin da shugabansu ya jagorance su suka duka a gaban shugaban ƙasar domin roƙon sa.

Shafin yaɗa labaru na Nile Post ya ruwaito shugaban ƙungiyar likitocin Dr Samuel Odongo Oledo na yaba wa shugaban ƙasar, wanda ya ce ya gyara harakar kiwon lafiya tare da inganta walwalar likitoci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending