News
A Chatham House, Tinubu ya wakilta El-Rufai, da wasu su amsar tambayoyin masu sauraro
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya kuma yin wani abu na daukar hankulan mutane a yau Litinin a Chatham House da ke birnin Landan, yayin da ya wakilci wasu daga cikin tawogarsa da su amsa tambayoyin da aka yi masa a wajen taron.
Tinubu ya je Chatham House ne domin tattauna wa da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje kan dalilin da ya sa a zabe shi a 2023.
Bayan gabatar da jawabinsa, wanda aka watsa kai tsaye ta gidan talabijin na Arise, wasu daga cikin mahalarta taron sun yi masa wasu tambayoyi da suka shafi tsaro, satar man fetur, ilimi da tattalin arziki da kuma yadda ya shirya magance rikice-rikice a yankunan idan ya zama shugaban kasa.
Yayin da mai jan ragamar taron ya tambaye shi da ya amsa tambayoyin, sai Tinubu ya kada baki ya ce zai sanya wasu daga cikin mukarraban sa su amsa tambayoyin.
Tsohon gwamnan jihar Legas ya baiwa gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna da ya yi bayani kan yadda gwamnatinsa (Tinubu) za ta magance matsalar rashin tsaro.
Sai kuma ya juya kan daraktan yada labarai na yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Dele Aleke domin amsa tambaya kan satar mai.
Tinubu ya kuma wakilta tsohon kwamishinan kudi a jihar Legas, Wale Edun, da ya amsa tambaya kan yadda shi (Tinubu) zai bunkasa tattalin arzikin kasar idan aka zabe shi.
