Connect with us

News

Zaɓen 2023: Atiku ya ce zai sayar da matatun man fetur

Published

on

Atiku abubakar

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen Najeriya na 2023, Atiku Abubakar ya ce zai sayar da matatun man fetur domin samar da kuɗin tallafa wa ƙananan sana’o’i.

Advertisement

Ba Ni Da Asusun Banki A Ko’ina Idan Ba A Najeriya Ba— Kwankwaso

A lokacin yaƙin neman zaɓe a Lagos, Atiku ya ce zai samar da kuɗi dala biliyan goma domin tallafa wa matasa su samu aikin yi.

A cewarsa “idan na sayar da matatar mai ta Fatakwal, da ta Warri da kuma matatar mai ta Kaduna.”

Advertisement

Bugu da ƙari a lokacin yaƙin neman zaɓen nasa, Atiku ya ce gwamnatin tarayya ce ta gina birnin Legas ba gwamnatin jiha ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending