News
Ghana za ta fara tura wa Birtaniya malaman jinya
DAGA MUHAMAD MUHAMAD ZAHRADDIN
Gwamnatocin Ghana da Birtaniya za su sanya hannu kan wata yarjejeniyar tura malaman jinya daga Ghana zuwa Birtaniya, wani abu da zai sanya Ghana ta samu ƙarin kuɗaɗen shiga da suka kai fan 1,000 a kan kowace malamar jinya ɗaya.
Ministan lafiya na ƙasar, Kweku-Agyeman-Manu ya shaida wa majalisar dokokin Ghana cewar “muna gab da sanya hannu kan yarjejeniyar, ciki har da waɗanda karatunsu ya tsaya a (ƙaramin) satifiket, za su je su samu horo sannan su dawo gida bayan shekara uku.”
A 2020 ma Ghana ta tura malaman jinya 100 zuwa tsibirin Barbados domin tallafa wa ƙasar wadda ke fama da ƙarancin malaman lafiya.
A baya dai shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya ce ƙasar na da wadatattun malaman jinya, har ma da rara, amma tura su asibitocin gwamnati na da wahala.
Sai dai shugabar ƙungiyar malaman jinya da ungo-zoma ta Ghana, Perpetual Ofori-Ampofo ta shaida wa BBC cewa ƙasar na fuskantar ƙarancin malaman jinya da za su yi aiki a asibitocin ƙasar.
Ghana na da malaman jinya masu rajista kimanin 120,000, amma kashi 46% ba su da babbar takardar karatu.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
