Connect with us

News

Ranar Masoya: Najeriya ce ta ɗaya a duniya a yawan masu bincike kan soyayya

Published

on

 

Shafin matambayi-ba-ya-ɓata na intanet mafi girma a duniya Google ya bayyana cewa Najeriya ce ta ɗaya a duk duniya a yawan mutanen da ke ziyartar shafin domin samun bayanai game da ranar Masoya ta Duniya

Advertisement

 

Jami’in hulɗa da jama’a da sadarwa na shafin mai kula da Afirka ta yamma Taiwo Kola Ogunlade ne ya bayyana haka.

Advertisement

Wata mata a kano ta nemi mijinta ya  sake ta don  ya hana ta  kudin birthday.

Ya ƙara da cewa bayanan da suka samu sun nuna irin jerin tambayoyi da masu amfani da shafin suka yi dangane da bikin ‘Ranar masoya ta Duniya’, kuma Najeriya ce ta kasance ta ɗaya a duniya a wannan shekarar ta 2023 da kashi 200 cikin 100.

 

Advertisement

Haka kuma rahoton ya nuna cewa a yanzu Najeriya ce ta farko da ‘yan ƙasarta ke neman bayanai game da soyayya a 2023, kuma tun 2004 ita ce ƙasar da ta fi kowacce bincike game da manhajojin da suka jiɓanci soyayya a duniya da saƙonnin Ranar Masoya da saƙonnin soyayya.

 

Advertisement

“A shafinmu na Google, manufarmu ita ce samar da bayanan da mutane ke nema a lokacin da suke buƙatarsu,” in ji ” Taiwo a cikin wata sanrwa da ya fitar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending