News
Zaɓen Najeriya 2023: Laifukan da za su iya kai ku gidan yari a ranar zaɓe.
Kamar a kowace kasa, dokar zabe ta tarayyar Najeriya ta tanadi hukunce-hukunce ga laifukan da ta bayyana cewa sun ci karo da yadda aka tsara gudanar da zabukan kasar.
Wasu daga cikin abubuwan da za a yi a lokutan zabe sun hada da damar cudanya da sauran jama’a da yin rajistar zabe da yin zaben kansa da kafa jam’iyyun siyasa da sauran su.
Taka irin wadannan tanade-tanaden na tattare da hukunce-hukunce, wadanda kan sa a dauki matakin ladabtarwa kamar cin tara da dauri, ko ma a aiwatar da duka biyun.
Bayan Ƙorafin da NNPP tayi An Sauyawa Kwamishinan Yan Sandan jahar Kano Wurin Aiki
Dokar zaben ta sanar cewa dukkan wani laifi da aka aikata karkashin wadannan tanade-tanaden sun shiga rukunin laifukan zabe.
Dukkan wadanda aka samu sun aikata wani laifi ko laifuka karkashin wannan dokar na iya fuskantar matakin kamawa da gurfanarwa a gaban kotu bayan jami’an tsaro sun gudanar da bincike kan lamarin.
Ga jerin wasu muhimman laifuka da dokar zaben Najeriya ta 31 ga watan Disambar 2018 ta tanada, kamar yadda Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Najeriya ta wallafa a shafinta.
1. Laifukan da suka shafi takardar kuri’a da akwatin zabe
Mallakar takardun kuri’a ba bisa amincewar dokar zabe ba da gurza takardar kuri’a ba bisa ka’ida ba da kuma hadawa da shigo da akwatunan zabe cikin Najeriya ba da amincewar dokar kasa ba.
Hukunci: Duk wanda aka samu da aikata wannan laifin zai fuskanci hukuncin tara ta Naira 50,000,000.00 ko dauri a kurkuku da bai gaza na shekara 10 ba ko ma a dora masa tarar da daurin.
2. Amfani da katunan zabe ba bisa ka’ida ba
Mika wa wani katin zabenka da niyyar ya kada kuri’a da shi yayin wani zabe ko kasancewa da katin zabe fiye da daya laifi ne a karkashin wannan doka ta zabe.
Hukunci: Duk wanda ya aikata wannan laifin zai fuskanci hukuncin tara ta Naira 1,000,000.00 ko dauri a kurkuku wanda ba zai gaza na wata 12 ba, ko ma a dora masa tarar da daurin tare.
3. Jigilar mutane a lokutan zabe
Daukan masu zabe a mota zuwa wata rumfar zabe a cikin motar gwamanti ko kwale-kwale na gwamnati laifi ne karkashin dokar zaben ta Najeriya.
Hukunci: Duk wanda ya aikata wannan laifin zai fuskanci hukuncin tara ta Naira 500,000.00 ko dauri a kurkuku wanda bai gaza na wata shida ba, ko ma a dora masa tarar da daurin tare.
4. Yin zaɓe ga wadanda ba su cancanci yin sa ba
Dukkan wanda aka samu yana kaɗa ƙuri’a ko ƙoƙarin kaɗa ta yayin wani zaɓe da hukumar zaɗe ta shirya duk da bai cancanci yin zaɓen ba ko kuma jan hankalin wani ya yi zaɓe alhalin bai cancanci yin zaɓe ba laifi ne ƙarƙashin wannan dokar.
Hukunci: Duk wanda ya aikata wannan laifin zai fuskanci hukuncin tara ta Naira 500,000.00 ko ɗauri a kurkuku wanda bai gaza na wata 12 ba, ko ma a ɗora masa tarar da ɗaurin tare.
5. Wasa da aiki ko sanarwa ko wallafa sakamakon zaɓe na bogi
Dukkan jami’in zaɓen da bai hallara a rumfar zaɓen da aka tura shi ya gudanar da zaɓe ba a kan lokaci ko wanda ya ƙi yin aikinsa kamar yadda doka ta tanadar ko kuma wanda ya sanar ko ya wallafa sakamakon zaɓe na bogi, dukkansu sun aikata laifukan zaɓe.
Hukunci: Duk wanda ya aikata wannan laifin zai fuskanci hukuncin tara ta Naira 500,000.00 ko ɗauri a kurkuku wanda bai gaza na wata 12 ba, ko ma a ɗora masa tarar da ɗaurin tare. Akwai kuma tanadin ɗaurin wata 36 ga wanda ya aikata lai fi na biyu a ƙarƙashin wannan sashen.
