Connect with us

News

Matakan Kariya Daga  Cutar Koda

Published

on

Masanin kiwon lafiya daga Jami’ar Ibadan, Dokta Yemi Raji, ya shawarci ’yan Najeriya da su rungumi matakan kariya a matsayin hanya mafi inganci wajen yaki da cutar koda.

 

Raji ya ba da shawarar hakan ne yayin zantawarsu da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ranar Alhamis a Ibadan,

An haramta wa Ahmed Al-Saleh kwallo har abada 

 

Shawarar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da duniya ke bikin Ranar Koda ta Duniya ta 2023 wadda aka saba gudanarwa duk shekara a watan Maris.

 

Ya ce, cutar koda ta zama babbar matsala ga kasashen duniya, kuma Najeriya ma ba ta tsira ba.

Advertisement

 

 

Masanin ya lissafo wasu matakan da za a kiyaye domin kauce wa kamuwa da cutar koda, ciki har da:

 

Kauce wa shan magani barkatai

Daina amfani da magani ba tare da umarnin likita ko masanin kiwon lafiya ba

Advertisement

Ziyartar asibiti duk lokacin da ake fama da wani rashin lafiya

A rungumi dabi’ar shan ruwa da yawa, saboda hakan na taimaka wa aikin koda

Takaita cin gishiri a abinci

Yawaita ta’ammali da ’ya’yan itatuwa

Guje wa yawan cin abincin gwangwani, da danginsa

Raji ya yi kira ga masu fama da cutar sukari da hawan jini da saura lalurorin da ka iya haifar da matsalar koda, da su ziyarci kwararrun wuraren da za su iya samun kulawar da ta dace.

Advertisement

 

(NAN)

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending