Connect with us

Politics

Ina Jiran Lokaci Domin Allah Shine Mai Bada Mulki —Hon. Bandirawo Dala

Published

on

 

 

Advertisement

Kwararre a fannin likitanci Kuma Dan gwagwarmaya a fannin ilimi, Jigo a Jam’iyar Action Democratic Party (ADP), dan takarar Majalisar jaha a Karamar Hukumar Dala, Sagiru Usman Bandirawoyace Ina jiran lokacine domin Allah Shine mai bada mulki

Jaridar indaranka ta rawaito cewa, yayin da a ke tunkarar kakar zaɓe ta 2023, ƴan takara da dama na jam’iyar APC da kuma NNPP dama PDP a karamar hukumar dala na nuna buƙatar su ta tsayawa domin wakilci na al’ummar karamar hukumar

Advertisement

Jihar Kano Ta Sake Samun Sabon Kwamishinan Yan Sanda.

Sai dai kuma, wannan jarida ta gano cewa kawo yanzu, ba a ga wata alama da ta nuna cewa dan takarar bazaiyi nassara ba a wannan lokacin

Amma, a wani shiri da tattaunawa da jaridar indaranka an jiyo Bandirawo na cewa ita magana ta siyasa ko muƙami, abu ne da Allah ne Ya ke yi.

Advertisement

A cewar Bandirawo, ban da Allah, babu wanda zai iya baiwa wani muƙami, inda ya ƙara da cewa duk wanda ya kaɗai kugen siyasa da wuri ya san Allah ne ke yi, haka-zalika wanda ya jira sai nan gaba shima ya san Allah ne ke yi.

“Ita maganar siyasa ko maganar muƙami, kowa dai ya san Allah ne Ya ke yi. Banda Allah ba bu mai yi kuma a kwai lokaci.

Advertisement

“Wanda ya buga kugen sa da wuri ya sani, wanda kuma ya bari ya jira lokacin Allah, shima kuma ya sani.

“Mu na jiran lokacin Allah, Allah kuma Shi ne mai yi,” in ji Hon Bandirawo .

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending