Politics
Nafi kowanne dan takarar majalisar jaha a Dala chanchanta-BANDIRAWO
Tsohon shugaban dalibai na Makarantar Kimiyya da Fasaha ta kano wanda aka fi sani da Bandirawo , wanda Kuma shi ne dan takarar majalisar jaha a Dala a jam’iyyar ADP yace duk cikin yan takarar majalisar jaha a karamar hukumar Dala yafi kowannen Dan takara chanchanta
Banderawo ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da wakilin jaridar indaranka a Kano.
Banderawo yace a batun wakilcin al’umma ana bukatar mutumin da yake da gogewa ya Kuma san matsalolin al’umma Kuma yasan hanyoyin da zai bi wajen magance matsalolin
Bandirawo Wanda yace wakilci kamar irin na majalisar jaha yana bukatar gogewa sosai wajen aiwatarwa fiye da na.majalisar jahar ” Kuma abatu takarar ana bukatar mutum Mai mutunci, mutum na matasa, mutum mai karrama mutane, ana da bukatar mutumin da shekarunsa suka kai kuma mutum mai Ilimi dai-dai gwargwado, Kuma al’umma suka San shi, to sai ka duba duk cikin Yan takarar da ake da su a Dala waye wanda zai baiwa Sha’aban abun da yake bukata idan ba ni ba”. A cewa Banderawo
Ya ce ya kamata mutane su sani sun dade suna bada gudunmawa a Siyasa ta hanyar wayar da akan mutane su zabi shugabanni da wakilai na gari, don haka yace suka ga dacewar a wannan karon suma su fito su gwada damar da kundin tsarin mulki kasa ya basu da kuma basirar da suke da ita.
Banderawo yace ya yi tanadi na abubuwan da zasu taimaka wajen ciyar da al’ummar dala gaba fiye da yadda suka Saba gani a baya.
