Ƙasashen Larabawa sun yi Alla-wadai da harin da sojojin Isra’ila suka kai Masallacin Kudus da kuma artabu tsakanin masallata da jami’an tsaro.
Babban Sakatare-janar na kungiyar ƙasashen larabawan, Ahmed Abdoul Ghiet, ya bayyana cewa, dabi’ar masu tsattsauran ra’ayi da ke kula da manufofin gwamnatin Isra’ila, za su haifar da rikice-rikice da Falasɗinawa matukar ba a kawo karshen su ba.
Zaben 2023 ne mafi karancin tashin hankali a tarihin Najeriya – Gwamnatin Tarayya
A yau, kungiyar za ta gudanar da wani taron gaggawa domin tattauna abubuwan da suka faru a birnin Kudus.
