Connect with us

Uncategorized

Sujjadar Cristiano Ronaldo bayan nasarar zura kwallo ta janyo cece-kuce

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Sujjadar Cristiano Ronaldo bayan zura kwallo a wasansu na jiya talata wanda Al Nassr ta yi nasara kan Ittihad da kwallaye 3 da 2 ya janyo cece-kuce a duniyar magoya bayan kwallo, lura da yadda tauraron ya yi salón murnar da ba a taba ganin wani wanda ba musulmi ba ya yi irinta walau bayan nasarar zura kwallo ko don wata murna daban.

Advertisement

Salon murnar kwallon na Ronaldo dai ya kayatar da dimbin magoya bayansa musamman a cikin kasar ta Saudi  Arabia da ya koma takawa leda a farkon shekarar nan bayan rabuwa da Manchester United.

Ronaldo ya yi sujjada bayan ya ci kwallo

Yayin wasan na jiya dai, Ittihad ta fara zura kwallaye 2 a ragar Al Nassr gabanin kwallon Ghareeb da Ronaldo bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne kuma ana kuma gab da tashi daga wasa Ronaldon ya zura kwallon ta 3 wadda ke nuna tabbacin ci gaba da kasancewar Al Nassr a saman teburin gasar ta Saudi Lig da tazarar maki 3 dai dai lokacin da ya rage wasanni 2 a kammala kakar bana.

Advertisement

Wasu faifan bidiyo dai sun nuna yadda dan wasan mai shekaru 38 bayan zura kwallon kamar yadda ya saba ya yi fitaccen salón murnar da aka fi sanin shi da ita wato SIUU sannan ya kara da sujjada lamarin da ya sanya ilahirin filin wasan karadewa da sowa.

Wannan murna ta Ronaldo dai ta zamo babban batun tattaunawa tare da tafka muhawara a dandalin sada zumunta.

Advertisement

Idan har Al Nassr ta iya nasarar doke Ettifaq a asabar mai zuwa kai tsaye kungiyar za ta dage kofin na Saudi Lig karo na 9.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending