News
Sanata Godswill Akpabio ya zama shugaban majalisar dattijai ta goma
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Godswill Akpabio ya yi nasara zama sugaban Majalisar Dattijan Najeriya bayan kaɗa ƙuri’a daga sabbin ‘yan majalisar.
Akawun majalisar dattijai ne ya bayyana sakamakon zaɓen da ‘yan majalisar suka kaɗa inda ya ce Sanata Godswill Akpabio ya yi nasara da rinjayen ƙuri’a 63.
Hukumar ICPC Ta Fara Gwanjon Kadarorin Data Kwace Daga Masu Karbar Rashawa
Inda ya kayar da abokin fafatawarsa Abdulaziz Yari wanda ya samu ƙuri’a 46.
Tuni dai akawun majalisar dattijan ya rantsar da sabon Shugaban Majalisar Dattijan, bayan ƙuri’un da ‘yan majalisa 109 suka kaɗa da safiyar yau.
Matakin ya zo ne bayan ƙaddamar da majalisa ta goma a ranar Talata.
Magoya bayan sabon shugaban majalisar dattijan sun yi ta sowa a zauren majalisar inda suka je suna rungume Sanata Godswill Akpabio.
Bayan kammala zaɓen sabon shugaban majalisar dattijain kuma, yanzu an shiga matakin zaɓen mataimakinsa
Nweze David Umahi ya gabatar da sunan Sanata Barau Jibrin a matsayin mutumin da yake son ganin an zaɓa a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattijai
