Connect with us

Business

Miliyoyin ‘Yan Najetiya Na Kara Zama Matalauta – WPC

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Hukumar da ke yaki da talauci ta duniya ta ce akwai ‘yan Najeriya miliyan 71 da ke fama da matsanancin talauci, kamar yadda bayanai suka nuna a shekarar 2023.

Hukumar mai suna The World Poverty Clock tana aiki domin gano yadda ake ci gaba da samun talauci a duniya.

Advertisement

Hukumar NAFDAC Ta Gargadi Al’umma Kan Wasu Magunguna Masu ‘Hadari’

Dan takarar gwamnan jihar Rivers na jam’iyyar APC, Tonye Cole, ya ruwaito bayanan da suka nuna cewa ‘yan Najeriya miliyan 71 na fama da matsanancin talauci kuma hukumar kididdiga ta kasa ta bayyana mutane miliyan 133 a matsayin wadanda ke rayuka a kasa da talauci.

Ya yi jawabi ne a wurin taron tattaunawa kan yunwa na Najeriya Zero a Abuja, wanda gidauniyar T200 ta shirya don bikin ranar yunwa ta duniya, ya kuma bayyana rahoton yadda ake fama da yunwa a Najeriya.

Advertisement

Cole ya kuma ambaci cewa sama da yara 10,000 da mutane 25,000 ne ke mutuwa a duniya kowace rana saboda yunwa, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Ya yi nuni da cewa, Najeriya na bukatar samar da tsari mai inganci, kuma mai dorewa, wanda zai zama mai saukin aiwatar da ayyukan kawar da fatara da kuma bin sa akan lokaci.

Advertisement

Ya ce, “Najeriya na da banbance-banbance na kasancewarta shelkwatar talauci a duniya, inda mutane miliyan 71 ke fama da matsananciyar talauci a yau (World Poverty Clock, 2023) da jimillar mutane miliyan 133 da suka kasance matalauta da yawa a cewar Hukumar Kididdiga ta Kasa.

“Kimanin mutane miliyan 828 ne za su farka a kowace rana ba tare da sanin inda za su samu abinci ba, kuma da yawa za su kwanta a ranar ba tare da sun ci komai ba. Wannan shi ne a cewar rahoton Majalisar Dinkin Duniya na 2021.

Advertisement

“Majalisar Dinkin Duniya ta kara da cewa a cikin wadannan mutane miliyan 828, 25,000 za su mutu a yau, ciki har da yara fiye da 10,000.

“Dole ne Najeriya ta tsara tsarin kawar da fatara mai sauki, kuma mai dorewa, sannan kuma ta tsaya tsayin daka akai.

Advertisement

Ya bayyana abubuwan da ke haifar da yunwa, yana mai cewa dole ne a dauki matakan magance wadannan matsalolin.

Ya ce “Sauran abubuwan da ke haifar da yunwa, kamar tashin hankali, rashin ƙarfin gwamnati, da tsarin kula da lafiya, dole ne a magance su cikin gaggawa idan har ana son a cimma magance Waɗannan matsaloli na gaske a Najeriya kuma magance su yana da mahimmanci ba kawai don kawar da yunwa ba har ma da ci gaban ƙasar gaba ɗaya.

Advertisement

“Gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu (GCFR) tana da kyakkyawan tanadi don inganta manufar karfafa tsarin dimokuradiyya wanda zai samar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar Najeriya.”

Rahoton Gidauniyar T200 ya nuna cewa Najeriya na fama da matsananciyar matsalar yunwa tare da maki 27.9 na yunwa a duniya, amma akwai gagarumin bambancin maki a fadin jihohi.

Advertisement

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Jihar da ke da maki yawan masu fama da mayunwata, tana da maki 44.2 ita ce jihar Yobe, inda ta samu maki 44.2, sannan jihar da ke da maki na biyu ita ce Sokoto, da maki 42.1.

Sauran jihohin da suke da maki sun hada da Zamfara, Kebbi, da Jigawa. Wadannan jahohin suna da yawan rashin abinci mai gina jiki da wofantar da yara.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending