News
Farashin Litar Man Fetur Ya Haura Naira 700 A Kauyen Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Al’ummar Najeriya da dama sun fara saita al’amuran su, domin dai tunkarar sauyin da zamani ya zo musu da shi na tsadar rayuwa da abubuwan gudanar da rayuwar.
Tsadar man fetur bayan cire Tallafinsa da gwamnatin tarayya tayi, ya kara taimakawa wajen sauya al’amura da dama.
A jihar Kano abubuwa sun fara sauyawa mazauna yankunan karkara, sakamakon yadda lamarin a wajen su yafi ƙamari.
Akan siyar da litar man fetur N550 a cikin birni, amma a yankunan karkara ba haka abin yake ba.
Wani kauye mai suna beli dake karamar hukumar rogo a jihar Kano jaridar indaranka ta iske yadda ake siyar da farashin kowace lita kan Naira 700 koma sama da haka a wasu wuraren.
Hakan ya sanya al’ummar yankin kira ga mahukunta domin taimaka musu, da nufin samar musu da mafita kan tsadar man.
Yawancin mazauna yankin babura ne da su masu kafa biyu, hakan ya sanya suke yawan shan man akai akai domin sufuri da Jigilar amfanin gona.
