Connect with us

News

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa (JAMB) ta sanya makin samun gurbin karatu a bana

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun jami’o’i ta kasa (JAMB) ta sanya maki 140 zuwa sama a matsayin makin samun gurbin karatu na shekarar 2022/23 a jami’o’in kasar nan.

Rijistaran hukumar Farfesa Is-haq Oloyede ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron shekarar 2023 kan shiga manyan makarantu da bayar da kyaututtuka da aka yi ranar Asabar din nan a Abuja.

Advertisement

CBN ya umarci bankuna dasu ringa karbar bayanan Kustomominsu da suka ha’da da shafin Mutum na Kafafen Sada Zumunta

Oloyede ya ce an amince da 100 a matsayin makin samun gurbin karatu a kwalejojin fasaha Polytechnics da Kwalejojin Ilimi.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Oloyede ya bayyana cewa abubuwan da aka ambata sune mafi ƙanƙanta, amma hakan ba yana nufin dole ne hukumomi su bi shi ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending