News
Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da kisan da aka yi wa wasu fararen hula Sudan
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da kisan da aka yi wa wasu fararen hula da ke barin birnin El Geneina da ke yammacin Sudan
Ofishin kula da yancin ɗan adam na Majalisar ya zargi dakarun RSF da masu tayar da ƙayar baya na yankin da kisan fararen hular.
Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa (JAMB) ta sanya makin samun gurbin karatu a bana
Dakarun RSF sun shafe makonni masu yawa suna faɗa da sojojin ƙasar, lamarin da ya tilasta wa fiye da mutum 500,000 barin muhallansu.
Majalisar Dinkin Duniyar ta ambato wani shaida da ya samu tsallakawa zuwa ƙasar Chadi yana tabbatar mata da harin.
Ya ce da yawa daga cikinsu sun ga yadda aka kwantar da mutanen da ba Larabawa ba a ƙasa kafin daga baya a harbe su.
BBC Hausa ta rawaito cewa Sannan suka warwatsa gawarwakinsu a kan titi a kusa da kan iyakar ƙasar.
Kashe-kashen da ake yi yanzu a yankin Darfur, ƙari ne a kan rikicin da yankin ke ciki tun 2003.
Kawo yanzu akwai alamun da ke nuna cewa faɗan ƙabilanci na ƙaruwa a Sudan.
