News
Buhari bai hana Tinubu binciken jami’an gwamnatinsa ba
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bai hana sabon shugaban ƙasar Bola Tinubu binciken jami’an gwamnatinsa ba.
Cikin wani saƙo da mai magana da yawun tsohon shugaban Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa ta twitter ya ce, labaran da ke yawo a shafukan sada zumunta, waɗanda ke cewa Buharin ya nemi Tinubu da kada ya binciki jami’an gwamnatinsa, labarai ne na ƙanzon-kurege.
Babu sulhu tsakaninmu da ‘yan bindiga – Gwamnatin Zamfara
Gabanin babbar salla ne Bola Tinubu ya gana da Buhari a wata ziyara da ya kai gidansa da ke Landan lokacin wata ziyarar ta ƙashin ƙai da Tinubun ya kai Landan bayan taron harkokin kuɗi na duniya da ya halarta a birnin Paris.
To amma Mallam Garba Shehu ya ce a lokacin ziyarar Buhari da Tinubun ne kawai suka gana babu wani mutum a ɗakin da suka gana, dan haka babu wanda ya san me suka tattauna.
Sanarwar ta kuma ce Buhari ya zaɓi fita daga Najeriya ne saboda gudun tsoma wa sabuwar gwamnati baki a al’amuranta.
”Da farko ya zaɓi ya zauna a gidansa da ke Daura domin samun hutu da nutsuwar da yake buƙata, to amma hakan bai samu ba, kasancewar a kullum, dare da rana, safe da yamma ɗimbin mutane ne ke ziyartarsa”, in ji Mallam Garba Shehu cikin saƙon da ya wallafa.
Ya ƙara da cewa tsohon shugaban ya tafi Landan ne domin samun hutun da yake buƙata, sannan kuma hakan zai bayar da dama ga sabuwar gwamnatin Tinubu ta gudanar da ayyukanta wajen cika alƙawuran da suka ɗaukar wa talakawan Najeriya.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
