News
Hukumar Hisba ta kama mutane biyu bisa zargin auren jinsi a Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Hukumar Hisba ta jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da yunkurin shirya auren jinsi.
Kwamandan Hisba, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar.
Sharuda Shida Da Sai Ka Cika Za A Saka Ka A Cikin Auren Zawarawan Kano
Ya ce a cikin wani faifan bidiyo, an ga wasu samari biyu mai suna Khalifa da Abubakar suna kokarin sumbata a yayin wani biki, wanda ake zargin bikin aurensu ne.
jaridar Daily post ta rawaito cewa Sai dai wadanda ake zargin sun musanta zargin cewa taron bikin ranar haihuwa ne ba bikin aure ba kamar yadda suka yi ikirari.
Advertisements
