Connect with us

News

Sharuda Shida Da Sai Ka Cika Za A Saka Ka A Cikin Auren Zawarawan Kano

Published

on

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Hukumar Hisbah karkashin jagorancin babban kwamanda  ta Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ta fitar da wasu sharuda da sai Maza da mata sun cika kafin shiga cikin shirin auren Zawarawa.

Jaridar kakaki  ta rawaito cewa Shirin auren zawarawan ya samu amincewar gwamnan jihar Kano injiniya Abba Kabir Yusuf.

Advertisement

Tsarin Raba Tallafin N8,000 Yaudara Ce — Uba Sani

Ga sharudan kamar haka

1- Ba mu bane zamu zabawa Mace ko Namiji wacce zasu yi auren tare. Dole sai sun daidaita tsakanin su kafin su iya zuwa mu basu form.

Advertisement

2 – Idan sun daidaita zasu ziyarci ofishin Hisbah, na kananan hukumomin su don yi musu tantancewa.

2a – Lafiya (gwaje-gwaje biyar kan lafiya)
b- Sana’a (Maza)
c- Halayyar su.
d- Saannan sai muyi musu bitar ilimin Aure da kuma koyawa mata sana’a da basu Jari.

Advertisement

3 – Dole wadanda zasu yi auren a tsakanisu sai sun zo da mutane biyu da zasu bayar da shaida a kan su kafin a yi musu aure a tsakani.

4 – Form din kyauta ne, kuma za a karba a ofisoshin Hisbah na Kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

Advertisement

5 – Idan ma’auratan suka cika dukkanin sharrudan nan da muka gindaya, to zamu aika musu da sako ta wayar salularsu.

6 – Kungiyoyin zawara na Kwankwasiyya, suma dukkanin su zasu sami wadanda suke so sai kuma su koma Kananan hukumomin su don a tantance su.

Advertisement

Hukumar Hisba ta jihar Kano ve ta fitar da wannan sanarwa aka rabawa manema labarai a Kano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending