Connect with us

News

An Ɗaura Auren Wata Budurwa Kan Sadaki Naira 1,000 A Kano

Published

on

FB IMG 1739227813121

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Wani matashi ya samu damar auren budurwarsa bayan ya cika sharadin da ta gindaya masa—na ɗaga wani mungureren ƙarfe da hannu ɗaya tare da biyan naira dubu ɗaya a matsayin sadaki.

Advertisement

Bayan matashin ya nuna ƙwarewarsa wajen ɗagawa, ya cika alkawarin bayar da N1,000 a matsayin kudin sadaki, inda suka nufi gidansu amaryar domin shafa addu’a. Wakilinta ya karɓi sadakin kuma aka ɗaura auren.

’Yan Uwan Juna Uku Sun Gurfana A Kotu Kan Dukan Miji Da Mata A Kano

A cewarsa, mahaifin amaryar yana wajen lokacin da ake tattaunawa amma bai ce uffan ba. Sai dai mahaifiyar amaryar ta bayyana cewa ba ta san da zancen ba.

Advertisement

Tuni dangin ango suka bayyana farin cikinsu, yayin da aka tsayar da ranar Laraba domin karɓar amarya.

Hukumar Hisbah ta ce aure ya halatta matuƙar mahaifi ya amince, amma idan ba haka ba, to ba shi da inganci.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending