News
JAMB Ta Gargadi Cibiyoyin Da Ke Yi Wa Dalibai Rajistar Jarabawa Da Dare Da Su Daina Haka
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’o’in Kasarnan, JAMB ta gargadi cibiyoyin yi wa dalibai rajistar jarabawar da su guji yin haka da dare.
Kakakin hukumar jarabawar Fabian Benjamin ya sanar da haka a wata sanarwa ranar Lahadi.
Benjamin ya ce hukumar na da masaniyar yadda wasu cibiyoyin ke yi wa dalibai rajista da dare.
Ya ce hukumar za ta dauki mataki mai tsauri domin hukunta duk cibiyar da aka samu na yin haka daga yanzu.
“Hukumar shirya jarabawar na da masaniya kan kokarin da cibiyoyin ke yi amma ba za ta lamunci a rika yi wa dalibai rajista cikin dare ba saboda tsaro.
Benjamin ya ce hukumar za ci gaba da sa ido domin ganin an kiyaye sharuddan da hukumar ta kafa yayin da ake wa dalibai rajistan jarabawar a kasarnan.
Benjamin ya ce cibiyoyin rajistan jarabawar da hukumar ke da masaniyar na yi wa dalibai rajista da dare sun hada da:
1. Jami’ar ‘Thomas Adewumi’ dake hanyar University Drive Off Oko-Idofin Road, Oko, jihar Kwara.
2. Cibiyar rajistan jarabawar dake Otukpo, lanba 14 layin Federal Road, Otukpo, jihar Benuwe.
3. Makarantar Ebenezer International dake lanba 23 layin Barry White kusa da karfe tafi da gidanka na Kamfanin MTN, Pipeline Rumukwurusi, Elimgbu a Fatakwal jihar Ribas.
4. Kolejin ilimi dake Gumel jihar Jigawa dake lanba 1 hanyar Kano dake Gumel jihar Jigawa.
5. Lafiagi Emirate Information Technology & Innovation Hub dake hannun riga da babban tashsr motoci a hanyar Emir’s Road, Lafiagi, jihar Kwara.
6. Zulqud Consult Ltd (ZCL CBT Centre) dake makarantar sakandaren dake Lugbe kusa da Car Wash, Lugbe Bridge Abuja.
7. Klinnicapps Academy, Old Imaje Road, Formerly Christian Secondary Commercial School, Okuku, Yala jihar Kros Ribas.
8. Kolejin Sani Mikaila Comprehensive dake Plot 34 Rikkos New Layout dake Jos jihar Filato.
Plateau State;
9. Beeps Technology Limited, 19 Obudu Street, Igoli, Ogoja jihar Kros Ribas.
10. FZX Media Consulting Limited, Km 15, Ikom-Ogoja Highway, Inside Havilla University, Nde, Ikom, jihar Kros Ribas
-
News7 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News3 days agoKotu Ta Daure Wani Limamin Masallacin Juma’a Wata 1 Kan Tura Bidiyon Tsaraici Ga Matar Aure A Kano
-
News5 days agoƘalubalen Da Masu Ƙananan Sana’o’i Ke Fuskanta Saboda Ƙarancin Wutar Lantarki A Kano
