News
Marken Mahuta: Kauyen Da Kalubalen Ilimi Da Rashin Lafiya Suka Addaba A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Marken Mahuta, wani ƙauye a karamar hukumar Ɗambatta, jihar Kano, yana cikin mawuyacin hali sakamakon rashin asibiti da makarantu masu inganci.
Tun shekaru aru-aru, al’ummar ƙauyen suna rayuwa ba tare da cibiyar lafiya ko makarantar da ke iya samar da nagartaccen ilimi ba. Wannan ya haddasa mace-macen mata masu juna biyu, yawaitar jahilci, da rashin kyakkyawar makoma ga matasa.
JAMB Ta Gargadi Cibiyoyin Da Ke Yi Wa Dalibai Rajistar Jarabawa Da Dare Da Su Daina Haka
Kalubalen Ilimi a Marken Mahuta
Rahoton KANO TIMES ya nuna cewa akwai wahala a neman ilimi a wannan ƙauye, musamman ga ‘yan mata.
“Babu wata yarinya da ta taɓa kammala firamare,” in ji Malam Bala, mazaunin ƙauyen. Maza kuma na fama da matsalolin rashin kayan aiki, kwararrun malamai, da wasu ƙalubalen al’adu.
Wata mahaifiya, Hajiya Sa’adatu, ta bayyana damuwarta:
> “Na yi mafarkin ganin ‘yata ta zama malama, amma wannan mafarki yana neman wargajewa. Babu malama mace a wannan ƙauye.”
Lafiya: Mata da Yara na cikin Hatsari
Rahotanni sun bayyana cewa ana yawan samun mace-macen mata masu juna biyu a Kano, inda mata 377.8 a cikin duk haihuwa 100,000 ke mutuwa.
A Marken Mahuta, mata masu nakuda suna rasa jariransu ko rayuwarsu saboda babu asibiti a kusa.
> “Mata masu juna biyu su ne mafi shiga tsananin wahala. Suna rasa rayukansu kafin su isa wani asibiti a Ɗambatta,” in ji Hajiya Binta.
Wata uwa mai suna Yalwa ta ce:
> “Ba mu da asibiti a ƙauyenmu. Lokacin da na yi nakuda, na gamu da ciwo mai tsanani, amma babu likita da zai taimake ni. A ƙarshe, na rasa jaririna.”
Rashin Hanya da Magunguna Masu Inganci
Idan lokacin damina ya zagayo, ƙauyen Marken Mahuta na komawa tamkar akurki, saboda babu hanyar shiga ko fita daga garin.
Hakazalika, mazauna ƙauyen na rayuwa ne ba tare da samun magungunan zamani ba, sai dai su yi amfani da na gargajiya.
Malam Yusuf ya ce:
> “Mun dogara ne da magungunan gargajiya da kantunan magani masu zaman kansu. Mun rasa cibiyar lafiya tun bayan da ta kone shekaru da suka gabata.”
Barazanar Cututtuka Masu Yaduwa
Zazzabin cizon sauro na ɗaya daga cikin manyan matsalolin rashin lafiya da ke addabar ƙauyen. Haka kuma, yara da yawa na mutuwa a lokacin damina saboda kamuwa da cututtuka.
Malam Sani ya ce:
> “Za a iya warkar da yara idan da akwai likita ko cibiyar lafiya mai inganci.”
Rashin Cika Alkawura Daga Gwamnati
A duk lokacin da aka ce siyasa ta zo, ‘yan siyasa na dafifin zuwa ƙauyen, duk kuwa da matsalar rashin hanya.
Duk da tarin alkawuran da suka yi, ba a sake gina cibiyar lafiya ba tun bayan konewarta, kuma ba a gyara hanyoyi ba.
Malam Bala ya ce:
> “Ko da muka roƙi taimako daga gwamnati, ba mu samu mafita ba. Har yanzu, babu wani cigaba da muka samu a gwamnatance.”
Mazauna Marken Mahuta na Neman Taimako
Mazauna ƙauyen sun yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni su taimaka wajen samar da asibiti, gyaran hanyoyi, da tallafa wa ilimin yara mata.
> “Ba damuwarmu samun alatun duniya ba ne, mu fatanmu samun abubuwan more rayuwa kamar su ilimi, kiwon lafiya, da hanya mai kyau,” in ji Malama Amina.
Rashin Jin Ba’asi Daga Hukumomi
Kokarin jin ta bakin Kwamishinan Lafiya na Kano, Dr. Abubakar Yusuf Labaran, da Kwamishinan Ilimi, Dr. Ali Haruna Makoda, ya ci tura.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto,
ba a samu wata sanarwa daga gare su ba game da matsalolin ƙauyen Marken Mahuta.
-
News7 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News4 days agoKotu Ta Daure Wani Limamin Masallacin Juma’a Wata 1 Kan Tura Bidiyon Tsaraici Ga Matar Aure A Kano
-
News6 days agoƘalubalen Da Masu Ƙananan Sana’o’i Ke Fuskanta Saboda Ƙarancin Wutar Lantarki A Kano
