News
A Yi Siyasa Cikin Mutunci Da Girmamawa – Waiya Ga ‘Yan Adawa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yi kira ga masu magana a gidajen rediyo, musamman ‘yan jam’iyyun adawa, da su rika yin adawa mai ma’ana cikin mutunci da girmamawa.
Waiya ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da masu magana a gidajen rediyo, ciki har da wakilai daga jam’iyyun siyasa daban-daban. Ya jinjinawa halartar su, yana mai cewa hakan ya nuna kishinsu ga jihar Kano, domin da ba sa kishin Kano, ba za su halarci taron ba.
Marken Mahuta: Kauyen Da Kalubalen Ilimi Da Rashin Lafiya Suka Addaba A Kano
A yayin jawabin nasa, ya jaddada mahimmancin adawar siyasa ta hanyar kaucewa kalaman da ba su dace ba. Ya ce duk da bambance-bambancen jam’iyya, wajibi ne a mutunta juna don inganta siyasa mai tsafta.
A wani bangare na kokarinsa na kyautata harkokin siyasa a Kano, kwamishinan ya sake nanata shirin farfado da kungiyar Gauta Club, wacce a baya ta taka muhimmiyar rawa wajen hada kan masu magana a gidajen rediyo ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ko ra’ayi ba.
Shugaban kungiyar Gauta a Kano, Alhaji Hamisu Danwawu Fagge, ya yabawa Kwamishinan bisa wannan kokari, yana mai cewa shirin zai taimaka wajen tsaftace harkar magana a kafafen yada labarai da kuma ci gaban Kano gaba daya.
-
News7 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News4 days agoKotu Ta Daure Wani Limamin Masallacin Juma’a Wata 1 Kan Tura Bidiyon Tsaraici Ga Matar Aure A Kano
-
News6 days agoƘalubalen Da Masu Ƙananan Sana’o’i Ke Fuskanta Saboda Ƙarancin Wutar Lantarki A Kano
