News
Nnamdi Kanu Ya Koma Hannun DSS Bayan Duba Lafiyarsa
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN.
Shugaban kungiyar IPOP masu fafutukar neman kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu ya koma hannun hukumar tsaro ta farin kaya DSS a ranar Lahadi, kwana guda bayan an sallame shi domin duba lafiyarsa da likitansa ya yi.
Idan za’a iya tunawa a ranar 20 ga watan Yuli ne babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar ta DSS da ta baiwa Kanu damar ganawa da likitocin sa, inda ta yi watsi da rashin amincewar DSS kan bukatar.
An Kashe Malamin Addini Da Manoma 5, An Sace Mutum 40 A Birnin Gwari
A cewar IPOB, ana zargin Kanu yana fama da ciwon kunne kuma yana bukatar tiyata.
Lauyan shugaban kungiyar ta IPOB, Ifeanyi Ejiofor, ya shaidawa manema labarai a ranar Lahadin cewa Kanu, wanda ke tsare tun 2021, ya samu damar ganawa da likitocinsa na kashin kansa, kuma an mayar da shi magarkama.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
