News
Tinubu ya sanar da ranar da zai rantsar da sabbin ministoci.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Shugaban kasa Bola Tinubu zai rantsar da sabbin ministocin sa da ya nada a ranar Litinin.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da ofishin sakataren gwamnatin tarayya (SGF) ya fitar.
Cire Tallafin: Jiigawa Ta Gabatar da Karin Kasafin Kudin 2023 Na Biliyan N44.7bn
An bayyana cewa za a gudanar da bikin ne a dakin taro na fadar gwamnatin jihar da karfe 10 na safe.
Daraktan yada labarai na ofishin SGF, William Bassey, wanda ya sanya hannu kan sanarwar, ya bayyana cewa ministocin za su zo da baki biyu kowanne.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai fadar shugaban kasar ta fitar da jerin sunayen sabbin ministoci da kuma mukamansu.
An nada Nyesom Wike a matsayin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), yayin da tsohon Gwamnan Osun, Gboyega Oyetola shi ne Ministan Sufuri.