Connect with us

News

Cire Tallafin: Jiigawa Ta Gabatar da Karin Kasafin Kudin 2023 Na Biliyan N44.7bn

Published

on

Gwamnan jahar Jigawa Alhaji Umar Namadi
Spread the love

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Majalisar zartaswa ta jihar Jigawa ta amince da kashe zunzurutun kudi Naira biliyan 44.7 a cikin shirin karin kasafin kudin 2023.

Advertisement

Kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na jihar, Babangida Umar Gantsa ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan sakamakon taron.

Tinubu ya fitar da jerin sunayen ma’aikatun ministocinsa

Ya ce karin kasafin kudin shi ne don samar da wasu muhimman ababen more rayuwa da ayyukan jin dadin jama’a a zango na 3 da 4 na wannan shekara.

Ya bayyana cewa bukatar kammala wasu ayyuka da kuma karin kudaden da gwamnatin tarayya ta yi sakamakon cire tallafin man fetur ya sa gwamnatin jihar ta yi karin kasafin kudi.

Advertisement

A cewar kwamishinan, wasu daga cikin sassan da za a samar da su daga karin kasafin kudin sun hada da ma’aikatar ayyuka da sufuri an ware mata tsabar kudi Naira biliyan (N13.8bn ),sai ma’aikatar lafiya (Naira biliyan N2bn), sannan ma’aikatar ilimi (Naira biliyan N3bn), kana ma’aikatar kudi (Naira biliyan 2.4bn) da kuma hukumar kula da tituna ta Jigawa (Naira biliyan N2bn).

Gantsa ya kara da cewa za a aika da karin kasafin kudin zuwa majalisar dokokin jihar Jigawa domin gudanar da ayyukan majalisa da amincewa.

A nasa bangaren, Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu Sagiru Musa ya bayyana cewa majalisar ta kuma amince da sama da Naira miliyan 192 domin fadada magudanun ruwa a karamar hukumar Kafin Hausa.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *