Connect with us

News

Dalilin Da Ya Sa Muka Jinkirta Biyan Fansho Sama Da Watanni Bakwai – Gwamnatin Jigawa

Published

on

Yan fansho a jahar Jigawa
Spread the love

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce an samu tsaikon biyan kudaden yan fansho na sama da watanni bakwai ne sakamakon kokarin da gwamnati ke yi na nazari da kuma karfafa shirin biyan kudin a jahar.

Sakataren zartarwa na shirin bayar da kudin fansho na kananan hukumomin jihar Jigawa, Alhaji Kamilu Aliyu Musa ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan biyan sama da naira biliyan biyu ga ma’aikata 746 da suka yi ritaya.

Advertisement

Gwamnan Jahar Yobe Ya Amince da Miliyan N667m don Biyan ‘Yan Fansho

Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da kwamitin kwararru da zai duba tare da gano dalilin jinkirin biyan ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya a jihar.

Musa ya tabbatar da cewa daya daga cikin dalilan da suka shafi tsarin biyan kudin shi ne fiye da kima daga ma’aikatan gwamnati.

A cewarsa: “Rashin aikin yi na tsawon shekaru ya gurgunta shirin sosai saboda yawan ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya sun haura kudaden da ake da su.

Advertisement

 

“Tun da farko mun kai rahoton matsalar ga tsohon gwamnan jihar, Gwamna Badaru Abubakar, a karshen wa’adinsa, inda ya kafa kwamitin, daga bisani Gwamna Namadi ya kaddamar da kwamitin bayan kammala zaben domin magance matsalar.

“Sashe na rahoton kwamitin ya hada da gano matsalolin shirin da samar da mafita ga matsalar.

Advertisement

“Daga yanzu, shirin zai ci gaba da biyan kudaden fansho a daidai lokacin da ya kamata ko kuma a kowace shekara.”

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *