Connect with us

News

Babangida Ya Bar Abin Alfaharin Da Ba Za A Taba Mantawa Da Shi Ba A Najeriya–Tinubu

Published

on

tsohon shugaban kasa na mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya)
Spread the love

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

Shugaba kass Bola Ahmad Tinubu ya taya tsohon shugaban kasa na mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya) murnar cika shekaru 82 a duniya.

Hakan na kinshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale, ya fitar.

Advertisement

Dalilin Da Ya Sa Muka Jinkirta Biyan Fansho Sama Da Watanni Bakwai – Gwamnatin Jigawa

ya ce shugaban kasa Bola Ahmad Tunibu ya yi farin cikin murnar bikin tare da iyalan tsohon shugaban, abokansa, da kuma abokan huldar sa.

Ya ce Babangida ya bar abin alfaharin da ba za a taba mantawa da shi ba na kare martabar kasa a lokacin yakin basasar Najeriya. Ya yaba da gagarumar gudunmawar da Babangida yake bayarwa wajen ci gaban kasa.

Ya ce hakan ya hada da samar da jihohi da dama don karfafa tsarin tarayya, samar da ababen more rayuwa, da walwala ga masana’antar watsa labarai da sauran tsare-tsare a sassan kiwon lafiya da tsaro. Ya lura da irin gagarumin matsayi na Babangida wanda bayan shekaru 30 a kan mulki, ya ci gaba da kasancewa muryar hikima da nasiha ga yawancin shugabannin siyasa na ciki da wajen

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *