Connect with us

News

Za Mu Cafke duk Wasu kwararrababbun Motoci Tare da Masu su – FRSC

Published

on

kwararrababiyar mota
Spread the love

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Shugaban hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC, Dauda Ali Biu, ya bayar da umarnin dakile duk wasu kwararrababbun motocin da ke yawo a fadin kasar nan.

Advertisement

Umurnin ya biyo bayan wani faifan bidiyo daya nuna wata tsohuwar motar da ke da matsalar injin da ke kan babbar hanyar tare da matacciyar taya guda daya daga cikin tayoyin baya na motar.

NDLEA ta nada Naira Merly shugaban yaƙi da shan miyagun kwayoyi

A cikin wata sanarwa da jami’in wayar da kan jama’a na hukumar, Bisi Kazeem, ya fitar, yace shugaban hukumar FRSC ya bayar da umarnin dakile irin wadannan tsoffin motoci nan take tare da damke masu su.

Sanarwar ta ce, motar mai lambar Legas AA07AG, ba tsohuwa ce kawai ba, amma tana tafiya ne da tayoyi uku kacal.

Advertisement

Biu ya ce an umurci jami’an hukumar da su sanya ido a kan motar da sauran motocin da ba su da kwanciyar hankali da ke bin manyan tituna a Najeriya, inda ya ce za a gudanar da aikin a duk fadin kasar.

Ya ce hukumar ta FRSC za ta hukunta mai ita da masu amfani da irin wadannan motocin.

 

Advertisement

Daily post 

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *