News
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da rage kashi 50% na kudaden rijistar ‘yan asalin Kano a manyan makarantun gaba da sakandare.
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
A wani gagarumin yunkuri na bunkasa harkar ilimi mai zurfi da kuma rage wa dalibai matsalolin kudi, Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya sanar da rage kashi 50 cikin 100 na kudaden rajista ga ‘yan asalin Kano da ke manyan makarantun.
Bayanin hakan ya fito ne a wani muhimmin taro da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano a yau Litinin , wanda ya hada shugabannin dukkanin manyan makarantun jihar.
Gwamna Inuwa ya bada umarnin rufe gidajen rawa a Jahar Gombe
Taron wanda Gwamna Yusuf da kansa ya jagoranta, ya samar da wata kafa ga masu ruwa da tsaki wajen yin shawarwari kan dabarun karfafa guraben karatu na manyan jami’o’i da kuma samar da sauki ga daliban Jahar kano.
Da yake gabatar da muhimman bayanai na sanarwar, kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Kano, Dakta Yusuf Kofar Mata, ya yi jawabi ga manema labarai a yau.
Gwamna Abba Kabir Yusuf a jawabinsa yayin taron ya jaddada muhimmancin ilimi mai sauki da kuma irin rawar da yake takawa wajen tsara makomar al, umma.
Ya kara da cewa rage kudaden rijistar wani mataki ne na ci gaba na samar da ilimi mai zurfi ga dimbin matasan Kano, wanda a karshe zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin jahar kano.
Gwamnan ya kuma bukaci daliban da su mayar da hankali da kyau wajen gudanar da ayyukansu na ilimi.
Ya jaddada cewa rage kudaden wata dama ce kawai ba har ma da alhakin da ya rataya a wuyan dalibai su mai da hankali kan karatunsu da ci gaban ilimi.