News
Kungiyar Tarayyar AfirkaTa Kira Taron Gaggawa Kan Juyin Mulkin Gabon
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Sojojin Gabon sun sanar cewa a ranar Laraba za su sanar da wanda zai jagoranci kasar, a yayin da kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta kira taron gaggawa kan juyin mulkin kasar.
Kwamandan rudunar tsaron shugaban kasar, Brice Oligui Nguema, ya sanar cewa Janar-janar din sojin kasar za su yi zama a ranar inda za su ayyana wanda zai jagoranci gwamnatin sojin.
Babbar matsalar dake damun matasa a wannan lokaci shine batun rashin aikinyi-Masani
Ya yi jawabin ne bayan hamɓararren Shugaban Gabon, Ali Bongo ya roƙi ƙasashen duniya su kawo ɗauki bayan sojojin ƙasar sun yi masa juyin mulki.
Sai dai wasu jama’ar kasar na ta murna inda suka fito kan titunan birnin Brazeville tare da sojojin suna rera taken kasar da kuma yaba wa sojojin bisa juyin mulkin.
Sojojin sun tsare Ali Bongo a Fadar Shugaban Kasa, inda daga nan ake kyautata zaton ya fitar da saƙon bidiyon da yake neman ɗaukin.
“Ina kira ga duk abokan ƙasarmu a faɗin da cewa su yi magana a kan abin da ke faruwa (…) kan waɗannam mutane da suka tsare Ni tare da iyalaina.” in ji shi a cikin bidiyon da aka gan shi cikin tsananin damwua.
Ya bayyana cewa ana tsare da shi ne a cikin gidansa, amma matarsa da ɗansa kuma suna tsare a wani waje daban.
Karon farko ke nan da aka ji ɗuriyar Bongo wanda sojoji suka hamɓarar ’yan sa’o’i bayan ya lashe zaɓen da zai fara wa’adin mulkinsa na uku, bayan ya gaji mahaifinsa a 2009.