News
Babbar matsalar dake damun matasa a wannan lokaci shine batun rashin aikinyi-Masani
DAGA FATIMA SULAIMAN SHU’AIBU
Bincike yayi nuni da cewa babbar matsalar dake damun matasa a wannan lokaci shine batun rashin aikinyi dake kara zama babbar barana atsakanin matasasn wannan ta sanya masu ruwa da tsaro da sauran Al’umma ke ta kiraye kiraye ga matasa dasu tashi tsaye suyi ruko da kana nan sana’oi domin dogaro dakai maimakon jiran gwamnati da ta Samar musu da abin yi.
cikin wani rahoto da Hukumar Kidayar Jama’a ta kasa tayi yayi hasashen cewa yawan al’ummar kasar nan ya kai miliyan 216.
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Amince Da Kasafin Kudi Naira Bilyan 44.7
Kiyasta yawan al’ummar da Najeriyar ke dasu a kan wannan adadi na mutane miliyan 216 dai, ya nuna kasar ta zama cikin jerin kasashen da suka fi samun karuwar jama’a a duniya.
Hakan dai na nufin al’ummar Najeriyar, na karuwa da sama da kaso uku cikin 100 a kowace shekara. uma ya yi
hasashen yana cewa fiye da kaso 60 cikin 100 na al’ummar Najeriyar matasa ne masu jini a jika,
wanda kuma kamata yayi hakan zama abin alfahari ga kasar ganin cewa yawan al’ummar abu ne mai matukar tasiri ga kasa kamar Najeriyar .
Sai dai kuma kusan za’a iya cewa abin ba haka yake ba sakamakon yadda matasan ke fuskantar kalubale ta kowace fuska abinda ke zama babbar barazana ga cigaban tattalin arziki.
Jaridar Indaranka ta rawaito cewa Mata da kanan yara ne suka fi fuskantar kalubale,
Abin da ya sanya masana ke bayyana hasashen cewa yawan al’ummar kasar da cewa akwai babban kalubale a tattare dasu.
Acewar Usman Yusuf Bala tsamiya babba mai sharhi kan al’ammuran yau da kullum anan kano dama kasa baki daya kasancewar Najeriyar na ajerin kasashen da ke kan gaba wajen yawan al’umma a nahiyara Afrika akwai bukatar mahukunta da su Samar da wani tsari da zai taimaki rayuwar matasa kasancewar matasan sune ginshin cigaban kowace al’umma to kamata yayi kafin ma su iya ba da gudummawarsu akwai buƙatar a
fara ba su gudunmawa.
Ya kuma cigaba dacewa abu ne a zahiri rashin aikin yi ya yi katutu a Najeriya a dalili tattalin arziki da ƙasar ta samu kanta.anzu idan ka duba a Najeriya ƙididdiga na nuna cewa rashin aikin yi ya kusa kai wa kashi 40 cikin 100. Kuma rawar da matasa ke takawa a harkokin siyasa ko shugabanci a Najeriya ba wata babba ba ce.
Amma kuma a cewarsa hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka, don kuwa akwai buƙatar sauran masu ruwa da tsaki su riƙawa gwamnatin domin kuwa yaƙin ya fi ƙarfinta ita kaɗai.
Masanin ya kuma nuna damuwa kan yadda gwamnatocin jihohi da yan kasuwa da bankuna ba sa tausaya wa matasan.
kuma ba sa riƙawa gwamnatin tarayya wurin agazawa matasa su sami abin yi.
A cewarsa ya kamata suma su fito da shirye-shirye da za su taimakawa matasa a matakin jihohi don ragewa gwamnatin tarayya aiki.
Ya kuma yi kira ga matasan da su rungumi noma da sauran sana’o’i a maimakon jiran aikin ofis.