Connect with us

Sports

Victor Oshimhen Ya Shiga Cikin Jerin masun neman kyautar Ballon d’Or

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

Hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF ta taya dan wasan Super Eagles Victor Osimhen murnar saka sunansa cikin jerin masun neman kyautar gwarzon dan wasan duniya ta Ballon d’Or ta shekarar 2023.

‘Yan wasa 30 ne ke takarar gwarzon dan wasa ta Ballon d’Or, wand a suka hada da Lionel Messi da Erling Haaland sai Kylian Mbappe da dai sauransu.

Advertisement

Na’urar Bibas Ce Kadai Aka Wajabta Ma Hukumar Zabe INEC Yin Aiki Da Ita – Kotu

A sanarwar da hukumar CAF ta fitar, ta taya Osimhen da Andrey Onana da Yassine Bounou da Mohammed Salah murnar kasancewarsu a cikin jerin yan wasan.

 

Advertisement

Osimhen ya taka rawar gani a kakar wasan da ta wuce kuma ya zura kwallaye uku a wasanni uku da ya buga a gasar Seria A ta bana. A yanzu haka yana tare da Super Eagles yayin da suke shirin tunkarar gasar neman gurbin shiga gasar AFCON da kasar Sao Tome da Principe a wasan da zasu yi ranar Lahadi.

Haka zalika itama Tauraruwar Super Falcons, Asisat Oshoala An saka ta cikin jerin masu takarar gwarzuwar yar wasa ta Ballon d’Or a bangaren mata na shekarar 2023.

Advertisement

 

Wani labarin kuma Rashin wutar lantarki da ake fama dashi tun kafin yanzu ya kara tsananta jiya a nan Jihar Kano, A yayin da kanfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO ya tsayar da aiyukansa kacokan, Lamarin da ya haifar da daukewar lantarki baki daya a cikin birnin Kano.

Advertisement

 

Wata sanarwa da shugaban sashin sadarwar kanfanin, Sani Bala Sani ya fitar, Ya alakanta daukewar wutar lantarkin da yin biyayya ga umarnin kungiyar kwadago ta kasa na tafiya yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyu.

Advertisement

 

Sanarwar da aka wallafa a shafin X na kanfanin, Ta baiyana cewar za’a cigaba da fuskantar matsalar daukewar wutar lantarkin, kasancewar yajin aikin gargadin zai ci gaba da kasancewa a yau Laraba.

Advertisement

 

Shima mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Kano, Kwamared Ado Riruwai, ya tabbatar da cewar kungiyarsu ta rufe dukkanin wasu ofisoshin gwamnati dake jihar Kano, domin tabbatar da yajin aikin gargadin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending