Connect with us

Sports

Cristiano Ronaldo ya ci kwallo ta 850 a tarihinsa

Published

on

Cristiano Ronaldo

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI.

Advertisements
Advertisements

Cristiano Ronaldo ya ci kwallo ta 850 a tarihinsa na kwallon kafa a wasan da Al Nassr ta doke Al-Hazm da ci 5-1 a gasar Saudi Pro League ranar Asabar.

Advertisements

Cristiano Ronaldo ya zura kwallonsa ta shida a wasanni uku da ya buga a baya-bayan nan sannan ya taimaka aka zura kwallo biyu a yayin da Al Nassr ta yi nasara sau uku a jere a gasar Saudi Pro League.

Advertisements
Advertisements

Gwamna Jahar Edo Ya Fitar Da Ofishin Mataimakinsa Daga Gidan Gwamnati

“Mun sake yin bajinta! Muna ci gaba da kwarewa. Mu ci gaba da tafiya @AlNassrFC…na ci kwallo 850 a tarihina kuma ina ci gaba da murza leda!” a cewar Ronaldo, mai shekara 38, a sakon da ya wallafa a soshiyal midiya.
Al Nassr na bayan kungiyar Al-Hilal da maki hudu a gasar lig bayan ta yi rashin nasara a wasanni biyu a wannan kakar wasa.
Ronaldo shi ne dan wasan da ya fi ci mata wasa a kakar da muke ciki inda ya zura kwallo shida, yayin da tsohon dan wasan Liverpool Mane yake biye da shi da kwallo biyar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending