Connect with us

Sports

Tawagar ‘Yan Wasan Super Eagles Ta Nijeriya Ta Koma Ta 44 A Fagen Kwallon Kafa A Duniya

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Nijeriya ta yi kasa zuwa mataki na 42 a jerin wadanda ke kan gaba a kwallon kafa a duniya kamar yadda hukumar kwallon kafa ta FIFA ta sanar.

Leadership ta ruwaito cewa A jadawalin da FIFA ta fitar ranar Alhamis, Nijeriya ta barar da maki 16.04, wadda ta hada 1474.44, wadda take da maki 1490.48 a cikin Oktoba, sai bi wannan koma bayan bai shafi matakin Super Eagles a nahiyar Afirka ba, har yanzu tana nan a matsayi na shida.

Advertisement

Wani mummunan hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar mutum a  hanyar jihar Kaduna zuwa Abuja

Biyan da Morocco da Senegal da Tunisia da Algeria da kuma Masar ke jerin wadanda ke kan gaba a iya kwallo a Afirka kuma wannan makin da Nijeriya ta barar ya biyo bayan tashi 1-1 da Lesotho da kuma Zimbabwe shima 1-1 a wasannin neman shiga gasar kofin duniya.

A fadin duniya kuma baki daya har yanzu Argentina ce ta daya a duniya, sai Faransa ta biyu da kuma Ingila ta uku a sahun farko-farko, yayin da Belgium ta yi sama zuwa mataki na hudu.

Advertisement

Brazil ta ci karo da koma baya, wadda ta koma ta biyar ta rasa gurbi biyu, hakan ya biyo bayan doke ta da Colombia da Argentina suka yi a wasannin shiga gasar kofin duniya a yankin Kudancin Amurka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending