Connect with us

Sports

Dan Kallo Ya Mutu Ana Tsaka Da fafata wasa a gasar La Liga

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

An dage wasan Granada da Athletic Bilbao a gasar La Liga ranar Lahadi, bayan da wani dan kallo ya mutu a filin wasa da ake kira Nuevo Los Carmenes.

Advertisement

Ana tsaka da wasa a minti na 18 a lokacin Athletic ta ci kwallo ta hannun Inaki Williams, sai aka dakatar da wasan.

Hukumar FRSC  Na Shirin Farautar Manyan Motoci Masu Dakon Dabbobi Hade Da Mutane

‘Yan kwallon sun fice daga filin a minti na 20 daga baya aka bukaci magoya baya da kowa ya kama gabansa.

Advertisement

 

Mahukuntan La Liga sun sanar da dage karawar ta kuma ce za ta sanar da ranar da za a sake fafatawar ta mako na 16.

Advertisement

Granada ta fitar da jawabi cewar ”An dage wasan nan take sakamakon da wani mai goyon bayanta ya mutu – tana kuma mika ta’aziyya da iyalansa.”

Magoya bayan Granada sun yi ta yi wa golan Athletic, Unai Simon tafi, bayan da ya je ya sanar da jami’ai mutuwar dan kallon.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending