Connect with us

Sports

Bournemouth ta kunyata Man United a Old Trafford

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Kungiyar Bournemouth ta je har Old Trafford inda ta lallasa Manchester United da ci 3 – 0 a gasar firimiya, nasarar da ta dada fito da irin matsalolin da suka addabi kungiyar a kakar bana.

Wannan rashin nasara ta dada jefa shakku a kan makomar Manchester wadda a baya ta zama gagara gasa a ciki da wajen Ingila, lokacin da Sir Alex Ferguson ya jagorance ta.

Wata Ɗalibar Jami’ar Nasarawa Ta Hallaka Kanta 

Dominic Solanke ya fara jefawa Bournemouth kwallonta ta farko a mintuna 5 da fara wasa, abinda ya taimake su tafiya hutun rabin lokaci suna da ci 1 – 0.

 

Advertisement

Bayan dawowa daga hutu, Philip Billing ya jefawa Bournemouth kwallonta na 2 a mituna 68, yayin da Marcos Senesi ya jefa ta 3 a mintuna 73.

 

Kafin tashi a wasan Bournemouth ta jefa kwallo na 4 a ragar Manchester, amma sai alkalin wasa ya kashe bayan an gano cewar kwallon ta taba hannun ‘dan wasan gaba na bakin.

Wannan gagarumar nasara ta taimakawa Bournemouth dada ficewa daga kasan tebur, inda yanzu take mataki na 13 da maki 19, yayin da Manchester ke rike da matsayi na 6 da maki 27

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending