Connect with us

Sports

Liverpool ta koma ta dayan teburin Premier League

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Liverpool ta doke Crystal Palace da ci 2-1 a wasan mako na 16 a gasar Premier League da suka kara a Selhurst Park ranar Asabar.

Advertisement

Palace ce ta fara cin kwallo ta hannun Jean-Philippe Mateta a bugun fenariti, bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu.

Wata Ɗalibar Jami’ar Nasarawa Ta Hallaka Kanta 

Daga baya Liverpool ta farke ta hannun Mohamed Salah, saura minti 14 lokaci ya cika, sai kuma Harvey Elliott ya kara na biyu a minti na 90.

Advertisement

Kwallo na 200 kenan da Salah ya ci a dukkan fafatawa, ya zama na biyar a Liverpool mai wannan kwazon.

Liverpool ce kan gaba a cin kwallo daf da za a tashi wasa fiye da kowacce kungiya mai kaso 40 cikin 100 tun bayan da Kloop ya karbi aikin horar da kungiyar.

Advertisement

Crystal Palace ta kammala wasan da ‘yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Jordan Ayew jan kati.

Da wannan sakamakon Liverpool ta dare mataki na daya a teburin Premier League da maki 37, bayan wasa 16.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending