News
Har Yanzu Samfurin Man Matatar Dangote Bai Fara Shiga Kasuwa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Matatar Dangote ba ta fara samar da ganga dubu 650 a kowace rana ba bayan wucewar ranar fara aiki da Matatar a watan Agusta, wanda Shugaban Rukunin Dangote, Aliko Dangote ya sanar a baya.
Idan dai za a iya tunawa, Dangote a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen kaddamar da matatar a hukumance a watan Mayu, ya ce, samfurin farko na ayyukan matatar zai kasance a kasuwa kafin karshen watan Yuli ko farkon watan Agusta na wannan shekara.
Mataimakin Gwamnan Jihar Edo Ya Fara Kwashe Kayan Offishinsa Daga Gidan Gwamnati
Duk da haka, babu wani digo na mai da aka tace daga matatar man da ya shiga kasuwa makonni bayan cikar wa’adin.
Da yake mayar da martani, shugaban kungiyar PENGASSAN, Festus Osifo, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta maida hankali wajen kammala matatun mai mallakinta domin Dangote dan kasuwa ne mai zaman kansa kuma zai iya yanke hukunci gobe cewa ba zai tace man ba.
Ya ce duk da cewa gwamnati na da kashi 20 cikin 100 na hannun jari a matatar, amma zaifi dacewa mu gyara namu matatun.
Wani labarin kuma Mataimakin Gwamnan Jihar Edo Ya Fara Kwashe Kayan Offishinsa Daga Gidan Gwamnati
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro