News
An Sake Samun Hatsarin Jirgin Ruwa A Jihar Adamawa

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ana fargabar mutane da dama sun mutu a karamar hukumar Fufore ta jihar Adamawa, a ranar Litinin, yayin da wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji ya kife.
Babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Adamawa, Dr. Mohammed Suleiman, ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda ya ce Lamarin ya faru ne da rana kuma ana ci gaba da aikin ceto.
Har Yanzu Samfurin Man Matatar Dangote Bai Fara Shiga Kasuwa
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Wannan Iftila’I na zuwa ne sa’o’i 48 bayan da mutane takwas suka mutu a wani hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Yola ta Kudu, yayinda akalla mutane 24 suka mutu a wani hatsarin kwale-kwale a jihar Neja ranar Lahadi.
Mahmud, wani masunci a yankin da ke cikin masu aikin ceto, ya shaidawa manema labarai cewa, za a iya hana aukuwar al’amarin idan fasinjojin sun yi amfani da rigar kariya tare da aiwatar da wasu matakai na kariya.
Wani labarin kuma Har Yanzu Samfurin Man Matatar Dangote Bai Fara Shiga Kasuwa
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro