News
Cutar Mashako Ta Kashe Mutum 453, A Nijeriya Cikin Wata 10
DAGA MUHAMMAD ZAHRADDIN
Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta kasa (NPHCDA) da hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa (NCDC) sun ce, an samu kesa-kesai da ake zargin cutar mashako guda 11,587 a Nijeriya, a cikin wannan adadin an tabbatar da 7,202 sun kamu da cutar a kananan hukumomi 105 kuma mutum 453 cutar ta kashe cikin wata goma kacal.
A wata sanarwar hadin guiwa da NPHCDA da NCDC suka fitar a ranar Litinin, sun ce jinkirin samun rigakafi shi ke janyo kamuwa da cutar musamman ga yara ‘yan shekara 5 zuwa 14 sannan sakamakon binciken rigakafin
Cutar mashako na kasa baki daya wanda ya nuna kashi 42 cikin dari na yara ‘yan kasa da shekaru 15 ne kawai ke samun cikakkiyar kariya daga cutar mashako.
Gwamnan Zamfara yace suna da hujjojin cewa Gwamnatin Tarayya na tattaunawar sirri da ƴan fashi
“Zuwa ranar 24 ga watan Satumban 2023, an samu rahoton kesa-kesai 11,587 kuma a ciki an tabbatar 7,202 sun kamu da cutar a kananan hukumomi 105 da suke jihohi 18 ciki har da babban birnin tarayya Abuja. Jihar da ta fi yawan wadanda suka kamu da cutar Kano ce mai adadi (6,185).
“Sauran jihohin da aka samu kesa-kesan su ne Yobe (640), Katsina (213), Borno (95), Kaduna (16), Jigawa (14), Bauchi (8), Lagos (8), FCT (5), Gombe (5), Osun (3), Sokoto (3), Niger (2), Cross River (1), Enugu (1), Imo (1), Nasarawa (1) sai kuma Zamfara (1).
“Mafi yawan wadanda suka kamu da cutar (5,299) kaso 73.6% an tabbatar ya kama yara ne da suke shekara 1 zuwa 14.
“Zuwa yanzu, adadin mutum 453 ne aka tabbatar cutar ta kashe,” a cewar sanarwar.
Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya ne ministan lafiya da walwalar jama’a Farfesa Ali Pate ya kafa kwamitin gaggawa na kasa, duba da yadda cutar ke kara ta’azzara da kuma gano cewa kashi 80 cikin 100 na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ba a yi musu allurar rigakafi ba ne.
Tawagar da ke karkashin jagorancin babban daraktan NPHCDA, Dr. Faisal Shuaib da darakta-janar na hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa (NCDC), Dr. Ifedayo Adetifa, da aka daura wa alhakin tsara ayyukan da za a bi wajen shawo man cutar da nemo mafita ta yadda za a samar da rigakafi yadda ya kamata.
Daga bisani hukumomin biyu sun bukaci iyaye da su tabbatar da an yi wa yaransu rigakafi domin karesu daga kamuwa da cutar ta mashako.