Connect with us

News

Ƙungiyar ƙwadago ta NLC za ta yanke shawara kan shiga yajin aiki

Published

on

kungiyar kwadago na zanga zanga

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Kungiyar Kwadago ta kasa NLC za ta gudanar da wani taron gaggawa na majalisar zartarwa ta kasa game da shirin da take yi na shiga yajin aikin sai baba ta gani.

Wannan matakin ya biyo bayan cikar wa’adin kwanaki 21 da ƙungiyar ta bai wa gwamnati don biya musu buƙatu.

Advertisement

Gwamnan Zamfara yace suna da hujjojin cewa Gwamnatin Tarayya na tattaunawar sirri da ƴan fashi 

A cikin wata takardar gayyata da ta tura wa manema labarai a yau Talata, NLC ta ce za ta gana da manema labarun a ranar ta yau domin tabbatar masu da matsayar da ta cimma.

Ƙungiyar dai a baya ta shirya yajin aikin gama-gari da ta gudanar a ranakun 5 da 6 ga watan Satumba, saboda tsadar rayuwar da ƙasar ta shiga sakamakon cire tallafin man da shugaba Bola Tinubu ya yi.

Advertisement

Bugu da kari, kimanin wata guda da ya gabata, ƙungiyar ƙwadagon sun shiga yajin aikin don magance irin matsalolin da suka shafi tsadar rayuwa, sai dai daga bisani suka dakatar da yajin aikin bayan tattaunawa da shugaba Bola Tinubu.

Wani labarin kuma Cutar Mashako Ta Kashe Mutum 453, A Nijeriya Cikin Wata 10

Advertisement

 

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

Advertisement

 

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

Advertisement

 

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

Advertisement

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending