News
Gwamnatin jihar Kano ta ce sama da yara 520 ne ake fargabar sun mutu sakamakon bullar cutar mashako
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Gwamnatin jihar Kano ta ce sama da yara 520 ne ake fargabar sun mutu sakamakon bullar cutar mashako a jihar.
Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Kano Dakta Muhammed Nasir Mahmoud ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake magana a taron wayar da kan ‘yan jarida na kwana daya kan bullar cutar mashako a jahar Kano wanda aka gudanar ranar Talata.
Ya ce tun bayan bullar cutar a watan Disambar 2022 jihar Kano ta samu mutane 8700 da ake zargin sun kamu da cutar inda 6300 aka tabbatar sun kamu da cutar.
Ya ce daga cikin kananan hukumomi 44 na jihar Kano, cutar mashako ta yadu zuwa kananan hukumomi 39 da cutar ta fi kamari inda ba a yi allurar rigakafin cutar ba.
A cewarsa, kashi 27% ne kawai aka yiwa allurar riga-kafin, kashi 7.5% an yiwa kashi 59.9% kuma kashi 5.5
Ya ce gwamnatin jihar Kano tare da goyon bayan gwamnatin tarayya suna aiki kafada da kafada domin kawo karshen cutar nan da Disamba, 2023.
Manajan kula da lafiya na UNICEF Dr. Serekeberehan S. Deres ya ce halin da yaran da ba a yi musu alluran rigakafi ba na da matukar muhimmanci, ba za a amince da su ba, kuma suna bukatar a gaggauta magance.
A cewar NCDC “Bayanan sun nuna, kashi 60.7 cikin 100 na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar mashako ba su da kashi daya, ma’ana ba a yi musu allurar kwata-kwata ba.”
Ya ce wasu daga cikin alamomin cutar sun hada da, ciwon makogwaro, wahalar numfashi ko saurin numfashi, zazzabi da sanyi.
Ya yi nuni da cewa, Najeriya na bukatar karfafa aikin rigakafi na yau da kullun zuwa dan magance wannan kalubale.
Don haka Dr Deres ya yi kira ga mahalarta taron da su kasance masu taka-tsan-tsan wajen wayar da kan masu hannu da shuni, da gwamnati, da iyalai, da al’umma, da kowa da kowa, kan mahimmancin rigakafin yau da kullum.
An bayyana cewa kashi 80 cikin 100 na masu cutar mashako an samu su a jihar Kano kuma 60.8
daga ciki yara ne.
